Ko kun san ana iya afuwa ga yan B*nd*ga dama sauran masu laifi, amma ta yaya za a iya yafe wa wadannan?

Da turanci ana ce mai (Prerogative of Mercy, da hausa kuma Afuwa) ga masu laifi.
A Najeriya, Afuwa (Prerogative of Mercy) wani iko ne da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya (wanda aka yi wa gyara a shekarar 1999) ya ba wasu manya domin su iya yin afuwa ko rage hukuncin mutumin da aka samu da laifi. Wannan iko ana amfani da shi ne domin hada adalci da jin qai a wasu yanayi na musamman.
Sannan kuma mutane Biyu ne kadai doka tabawa damar yin wannan afuwar, amma kafin nan ga wani dan Qarin haske a kan shi wannan Afuwa;
Da farko de menene wannan afuwar?
Wannan afuwar de tana nufin a sauke wa mutum laifi kuma a wanke shi daga wannan laifin (Discharged and acquitted) ya zama kamar haifaffen sabon jinjiri, kwarai ba laifin kome a kansa.
kuma sake bude wannan shariar shima laifi ne domin doka ta hana a sake gurfanar da mutumin da aka taba gurfanarwa a gaban kotu a kan wani laifi da ita kotun kanta ko watan ta tayi shiria a kan sa ana kiran wannan (Autrefois convict)
Wannan afuwa ana iya yin sa a kan ko wane irin laifine idan mutum ya aikata shi kuma kotu ta zaratar mai da hukunci bayan ta sameshi da laifi.
Shin suwaye za a iya yi wa wannan afuwa ta (Prerogative of Mercy)
Ko mai satan mutane, ko dan ta’adda, ko dan fashi, kai koma dan menene.
Wadannan mutanen guda biyu da zan lissafa muku suna da ikon yi musu afuwa kuma ba abinda zai faru
1) na farko shine Shugaban Ƙasa
A qarqashin Sashi na 175 na Kundin Tsarin Mulki, Shugaban Qasa yana da ikon amfani da Prerogative of Mercy ga mutanen da aka samu da laifukan da suka shafi dokokin Tarayya.
Kafin ya yi amfani da wannan iko, dole ne ya tuntuɓi Majalisar Shawarar Ƙasa.
2) Gwamnan Jiha
A qarqashin Sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulki, Gwamnan Jiha yana da irin wannan iko kan mutanen da aka samu da laifukan da suka shafi dokokin jiharsa.
Kafin ya yi amfani da wannan iko, dole ne ya tuntuɓi Kwamitin Shawara kan Afuwa na Jiha.
Shin ko kun san Wadanne Irin Afuwa Za Su Iya Yi?
Shugaban Qasa ko Gwamna na iya:
1) Ko wanne daga cikin su na iya yin cikakkiyar afuwa ga wanda aka yanke wa hukunci.
2) Da kuma yin afuwa mai sharadi, wato afuwar da aka daura wa wasu sharudda.
3) Ko Jinkirta aiwatar da hukunci na wani lokaci ko har sai an sake yin wani hukunci.
4) Sauya hukunci mai tsanani zuwa mafi sauqi, misali rage hukuncin dauri na dogon lokaci zuwa gajere.
5) Rage ko sauke hukunci, ko tara ko qwace dukiya gaba ɗaya ko wani ɓangarensa.
Shin a Waɗanne Yanayi Ake Yin wannan afuwa ta (Prerogative of Mercy)?
Duk da ya kasance Kundin Tsarin Mulki bai lissafo dukkan yanayin da za a iya amfani da shi ba, ana yawan amfani da wannan iko idan:
1) Wanda aka yanke wa hukunci ya tsufa qwarai.
2) Ko Yana fama da rashin lafiya mai tsanani ko mara magani.
3) ko idan Ya nuna nadama kuma ya gyara halayensa.
4) ko idan Hukuncin ya yi tsauri fiye da yadda ya dace.
5) ko idan Yin afuwa zai amfani al’umma ko ya taimaka wajen samar da zaman lafiya.
6) ko idan Akwai dalilan jin qai ko na dan Adam.
7) Ko idan Ci gaba da daurin ba zai kara amfani ga adalci ba.
Amma ta Yaya Ake Samun Wannan Afuwa?
To yawanci de ga hanyoyin da ake bi domin samun wannan afuwar;
1) A gabatar da buqatar afuwa ga hukuma.
2) Kwamitin da ke kula da Afuwar ya binciki lamarin.
3) Kwamitin ya miqa shawararsa ga Shugaban Qasa ko Gwamna.
4) Shugaban Ƙasa ko Gwamna ya yi shawarar da ta dace bayan tuntuɓar majalisar da doka ta tanada.
5) Idan an amince, sai a fitar da takardar hukuma ta afuwa, ko rage hukunci ko sauya hukunci.




