Haqqoqin Dan Adam

Shin akwai banbanci tsakanin wurin da ake shariar yara da ake zargi da aikata laifi da na manya?

Kafin nan de waye ma yaro a dokar najeriya? Kuma a shekara nawa laifi yake fara hawa kansa?

A qarqashin juvenile justice system shekarar mallakar hankali a qasar Najeriya yana farawa ne a lokacin da mutum ya cika shekara goma sha takwas (18).

Eh, kwarai akwai Kotun Yara a Najeriya ana kiranta da (Juvenile Court da kuma Family Court)

Ba kowane yaro da ya aikata laifi ake kaiwa kotun manya ba. Dokokin Najeriya sun tanadi kotu ta musamman domin sauraron shari’o’in yara, tare da kare mutuncinsu da kuma ba su damar gyaran hali maimakon hukunci mai tsanani.

Ga cikakken bayani tare da hujjojin doka masu inganci a kan kotun yara.

Kotun Yara (Juvenile Court) ita ce kotu ta musamman da aka kafa domin sauraron shari’o’in da suka shafi yara wadanda shekarun su ya gaza goma sha takwas (18).

A wannan kotu ana kula da jin dadin yaro, ana kuma tabbatar da cewa an kare masa haqqoqinsa kamar yadda doka ta tanada.

A cikin duk wata qasa da ta ke da yarjrjeniya da majalisar dinkin duniya tana amfani da Child Rights Act, 2003, amma ko wace qasa da irin nata baizama lallai abinda aka rubuta a qarqashin dokokin Najeriya ya zama daya da wata qasa.

Babban dalilin kafa Kotun Yara shi ne

1) kare yara daga shiga tsarin shari’ar manya

2)domin bincike ya nuna cewa haɗa yaro da manyan masu laifi na iya sa ya qara lalacewa maimakon ya gyaru.

Saboda haka, doka ta fi mayar da hankali kan:

a) Gyaran hali.
b) Ba da shawara.
c) Kare haqqin yaro.
d) Sake dawo da yaro cikin al’umma.

Kotun yara na sauraran ko wane irin qararrakin da suka daganci yaran da basu haura shekara goma sha takwas ba (18) amma ga wasu daga cikin ire iren su a nan qasa;

1) Shari’o’in yara da ake zargi da aikata laifi.
2) Shari’o’in cin zarafin yara.
3) Shari’o’in kula da tarbiyya da walwalar yara.
4) Shari’o’in reno da kula da yaro.
5) Duk wata shari’a da ta shafi kare muradun yaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button