Haqqoqin Dan Adam

Abubuwa 15 da Doka Ta Ba Wanda Aka Kama… Amma Mutane Da Yawa Ba Su Sani Ba!

Shin ko kun san wa’enne Haqqoqi ne doka ta tanadar wa mutum Wanda Ake Zargin ya aikata laifi a Najeriya?

Da farko de kusani shi wannan ya bambamta da haqqin dan Adam wanda majalisar dinkin duniya ya lissafa, da kuma wanda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar wa mutun, Chapter 4.

Daga lokacinda akace an kama mutum da zargin aikata wani laifi wanda yayi karo da dokokin kasa to wadannan haqqoqin sun sauka daga kansa se kuma wannan wanda zan zayyana muku a nan kasa.

1) Haqqin Sanin Dalilin Kama Shi

Dole ne jami’an tsaro su sanar da wanda suka kama dalilin kamarsa cikin harshen da yake fahimta.

2) Haqqin Yin Shiru

Wanda ake zargi yana da haqqin yin shiru, kuma ba za a tilasta masa ya faɗi abin da zai iya cutar da shi ba.

3) Haqqin Samun Lauya

Yana da haqqin ya nemi lauya wanda zai kare shi kafin ya ba da bayani ko a ci gaba da bincike.

4) Haqqin Yanci

Ba a yarda a tsare mutum ba tare da izinin doka ba. Dole ne a kai shi gaban kotu cikin lokacin da doka ta tanada.

5) Haqqin Beli (Bail)

Idan laifin yana cikin waɗanda ake bayar da beli, yana da haqqin neman beli daga ’yan sanda ko kotu.

6) Haqqin Mutunci

Ba a yarda a doke shi, a azabtar da shi, ko a wulakanta shi ba. Dole ne a mutunta mutuncinsa.

7) Haqqin Shari’a ta Adalci

Yana da haqqin a saurari shari’arsa cikin gaskiya da adalci a gaban kotu mai zaman kanta.

8) Ana Ɗaukarsa Mara Laifi

Doka tana ɗaukar wanda ake zargi mara laifi ne har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.

9) Haqqin Sirri

Doka tana kare sirrin rayuwarsa da hanyoyin sadarwarsa, sai dai idan doka ta ba da damar bincike.

10) Haqqin Samun Kulawar Lafiya

Idan yana buƙatar magani ko ya ji rauni yayin da yake tsare, dole ne a ba shi kulawar lafiya.

11) Haqqin Tuntuɓar Iyalansa

Yana da haqqin ya sanar da iyalansa, abokinsa ko wani da ya amince da shi cewa an kama shi.

12) Haqqin Mai Fassara

Idan bai fahimci harshen da ake amfani da shi ba, yana da haqqin a samar masa da mai fassara.

13) Haqqin Kada a Tilasta Masa Furta Laifi

Ba a yarda a tilasta masa ya amsa laifi ta hanyar duka, azabtarwa ko barazana ba.

14) Haqqin Kalubalantar Tsare Shi Ba Bisa Ka’ida Ba

Idan an kama ko an tsare shi ba bisa doka ba, yana da haqqin ya garzaya kotu domin neman a sake shi da kuma neman diyya idan ya dace.

15) Haqqin a Kammala Shari’arsa Cikin Lokaci Mai Ma’ana

Doka tana buƙatar a gudanar da shari’ar wanda ake zargi ba tare da jinkiri marar dalili ba.

Toh daga karshe de zamu rufe da wannan

Mutum yayi duk qoqarin da zaiyi kar ya aikata laifi, kumafa bayan wannan akwai haqqoqin wanda aka yankewa hukunci, shima wani abu ne na daban.
Mun gode da ziyartar shafin mu na Farfajiya.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button