Shin Zargi Ko Gurfanarwa Na Nufin Mutum Ya Rasa Dukkan Haqqoqinsa?

Aa gaskiya ziyarci Farfajiya.com domin samun cikakken bayanqi da hujjoji na sharia a kan wannan da ma ire ireshi.
Haqqoqin Wanda Aka Gurfanar a Kotu a Ƙarƙashin Dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya
1) Haqqin dole se anyi Masa Shari’a Mai Adalci
Dole ne kotu ta saurari shari’arsa cikin gaskiya, da adalci ba tare da nuna son kai ga kowane ɓangar ba.
2) Haqqin Ɗaukar Sa a matsayin Mara Laifi Har Sai An Tabbatar da Laifinsa
Ba a ɗauke shi mai laifi ba sai bayan kotu ta tabbatar da hakan ta hanyar gamsassun hujjoji da aka gabatar a kan shi kuma bashi da gamsassun hojjojin da zasu wanke shi a kan tuhuma da kuma hujjojin da aka gabatar a kansa.
3) Haqqin Sanin Tuhumar da Aka Gabatar a Kansa
Dole ne a bayyana masa tuhumar da ake yi masa cikin harshen da yake fahimta.
4) Haqqin Samun Isasshen Lokaci Don Shirya Kariyarsa
Ya kamata a ba shi lokaci da damar tattara hujjoji da shaidunsa.
5) Haqqin Samun Lauya
Yana da damar zaɓar lauyansa ko kuma a tanadar masa da lauya idan doka ta buƙata kuma shima wanda za a bashin se idan ya aminta dashi, wato bazaiyuwu a tilasta masa ba.
6) Haqqin Halartar Shari’arsa
Bai a kamata a yi masa shari’a ba tare da kasancewarsa a wurin ba, sai a lokutan da doka ta amince.
7) Haqqin Tambayar Shaidun Masu Ƙara
Yana da damar tambayar shaidun da akai ko kuma ake amfani da su a kansa.
8) Haqqin Kawo Shaidunsa
Yana da damar gabatar da shaidu da hujjojin da za su kare shi.
9) Haqqin Samun Mai Fassara
Idan bai fahimci harshen kotu ba, dole ne a ba shi mai fassara kyauta, wannan musamman wurin yarukan kotu wanda ba turanci bane ba ana ce musu “Legal maxims ko kuma lain maxim”.
10) Haqqin Yin Shiru
Ba za a tilasta masa ya amsa laifi ko ya bayar da shaidar da za ta cutar da shi da kansa ba.
11) Haqqin a Yanke Hukunci Cikin Lokaci Mai Ma’ana
Bai kamata a jinkirta shari’arsa ba tare da dalili na doka ba.
12) Haqqin Ɗaukaka Ƙara
Idan bai gamsu da hukuncin da kotu ta yanke masa ba, yana da damar ɗaukaka ƙara zuwa babbar kotu. Musali daga (kotun majistre zuwa kotun Jaha, ko ta kasa, ko kuma daga kotun jaha zuwa kotun daukaka kara.) amma fa wannan yana aiki ne idan ba sharia ce da aka yanke ta a kotun koli ta qasa ba. Wacca ake yi wa laqabi da kotun Allah ya isa.
13) Haqqin Samun kwafin hukuncin kotu
Yana da damar samun kwafin hukuncin kotu domin ya fahimci dalilan hukuncin ko ya ɗaukaka ƙara.
14) Haqqin kar a Sake Yi Masa Shari’a Kan Laifi Ɗaya
Idan kotu ta riga ta yanke hukunci na ƙarshe a kan wani laifi, ba za a sake gurfanar da shi a kan wannan laifi ɗaya ba.
Wato idan ya kasance an zargi malam Az da satan Naira dari biyun Malam Bz, har aka gurfanar da Malam Az a gaban kotu ta yanke mai hukunci ko kuma ta wanke shi daga zargin da akayi masa fa, to wannan shariar ta kare wato baza a sake budeta a wata kotu da sabon tuhuma kamar yadda akayi na farko ba sede a daukaka kara. Idan an aikata haka ana kiran shi a yare doka “Autrefois convict”.
15) Haqqin Samun Diyya Idan An Yi Masa Rashin Adalci
Idan aka tabbatar an hukunta shi bisa kuskure, yana iya samun diyya kamar yadda doka ta tanada.
Ka cigaba da bibiyar Farfajiya.com domin samun ire iren wadannan.




