Shin ko kun san babu gidan Yari a Najeriya?

Eh kwarai Babu gidan yari a karsar Najeriya a yanzu haka.
Kuma ga bayani tare da hujjoji masu ma’ana wadanda suka zayyana hakan, kaci gaba da bibiyar Farfajiya.com domin samun ire iren wadannan.
Da farko zamu fara da Haqqoqin Fursunoni a Ƙarqashin Dokokin Najeriya
Mutane da yawa suna tunanin cewa idan an tsare mutum a gidan gyaran hali, to ya rasa dukkan haqqoqinsa. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Dokokin Najeriya, musamman Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya gyarrare a 1999 da kuma Dokar Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (Nigerian Correctional Service Act, 2019) sun tanadi cewa dole ne a mutunta haqqoqin fursunoni.
Dokar Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (Nigerian Correctional Service Act, 2019) ta zayyana cewa tun daga lokacin an sauya sunan gidan yari izuwa Gidan Gyaran Hali, wanda wannan shima ci gaba ne mai kyau kwarai.
Ga wasu daga cikin muhimman haqqoqin fursunoni:
- Haqqin Rayuwa
Kowane fursuna yana da haqqin rayuwa, kuma dole ne hukumomin gidan gyaran hali su kare rayuwarsa.
- Haqqin Mutunci
Ba a yarda a azabtar da fursuna ko a yi masa wulakanci, ko acimasa zarafi ko mu’amalance shi cikin wulakanci ba.

- Haqqin Samun Kulawar Lafiya
Fursuna yana da haqqin samun magani da kulawar lafiya idan ya kamu da rashin lafiya ko wane iri ne kuma a kyauta du tsadan sa kuwa.
- Haqqin Samun Abinci da Ruwan Sha
Dole ne a ba fursunoni isasshen abinci mai gina jiki da kuma tsaftataccen ruwan sha.
- Haqqin Muhalli Mai Tsafta
Ya kamata a samar musu da wurin zama mai tsafta, da iska mai kyau da kuma kayan tsafta.
- Haqqin Samun Lauya
Fursuna yana da haqqin yin magana da lauyansa, musamman idan yana da shari’a a kotu.
- Haqqin Shari’a Mai Adalci
Idan har shari’arsa ba ta kammala ba, yana da haqqin a yi masa shari’a cikin adalci.
- Haqqin Addini
Kowane fursuna yana da haqqin yin ibadarsa da bin addininsa muddin hakan bai karya dokokin gidan gyaran hali ba.
- Haqqin Ganin Iyalai
Doka ta ba fursuna damar karbar baki da yin hulɗa da iyalansa bisa qa’idodin gidan gyaran hali.
- Haqqin Ilimi da Koyon Sana’a
Ana ba fursunoni damar yin karatu da koyon sana’o’i domin su gyara rayuwarsu bayan sun fito, da wannan yanzu akwai fursunoni masu digiri a gidan yari har ma masu matas, har ma fannin addini ba a barsu a baya ba, suna da mahaddata Qurani.
- Haqqin Gyaran Hali dan Komawa Cikin Al’umma
Babban manufar gidan gyaran hali ita ce gyaran hali, ba azabtarwa kawai ba. Saboda haka ana shirya fursunoni domin su koma cikin al’umma su zama mutane nagari.
- Haqqin Kai Ƙorafi
Idan an tauye masa haqqinsa, fursuna yana da damar kai ƙorafi ga hukumomin da abin ya shafa,
Yawwa wannan ya qunshi cewa har kara yana iya shigarwa a kan abokan zaman sa koma ma’aikatan gidan, a cikin gidar har ma wajen gidan idan ta kama.
- Haqqin Raba Fursunoni Bisa Matsayinsu
Doka ta tanadi a raba:
a)Waɗanda ake jiran shari’arsu da waɗanda aka yanke wa hukunci.
b) Maza da mata.
c) Yara da manya.
d) matakin taifuka
e) tsawon lokacin da zasu zauna a gidanmusali
-wani dan gajeren lokaci ne
-wani dogon lokaci,
-wani rayuwar sa gaba daya a ciki zai karar a ciki
-wani kuma kasheshi za ayi a ciki kawai lokaci yake jira.
- Haqqin Neman Beli (Ga Waɗanda Ake Jira a Yi Musu Shari’a)
Idan doka ta amince, wanda ake tsare da shi yana da haqqin neman beli kafin a yanke masa hukunci.
- Haqqin Daidaito
Ba a yarda a nuna wa fursuna wariya saboda qabila ko, addini ko, harshe ko, jinsi ko wani matsayi ba.
Daga karshe de inaso ku gane;
Dokokin Najeriya sun tabbatar da cewa daure mutum ba yana nufin ya rasa dukkan haqqoqinsa ba. Duk da cewa an dakile masa yancin zirga-zirga, har yanzu yana da haqqin rayuwa, mutunci, lafiya, ilimi, addini, adalci da sauran haqqoqin ɗan Adam. Hukumomin Nigerian Correctional Service suna da alhakin kare waɗannan haqqoqi tare da taimaka wa fursunoni su gyara rayuwarsu kuma su koma cikin al’umma cikin mutunci.
Kucigaba daga bibiyar Farfajiya.com




