Haqqoqin Dan Adam

Kafin Ka Ce Ba Ka Da Haggi… Karanta Wannan!

Haggogin Asali da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar alif dubu daya da dari tara da casain da tara (1999) Ya Tanada;

1) Haggi na Rayuwa (sashi na 33)

Kowane mutum yana da haggin rayuwa. Ba a yarda a kashe mutum ba sai a lokutan da doka ta amince da su.

2) Haggi na Mutunci (sashi na 34)

Kowane mutum yana da daraja da mutunci. Ba a yarda a azabtar da mutum, a wulakanta shi, ko a mai da shi bawa ba.

3) Haggi na ’Yanci (sashi na 35)

Kowa yana da haggin rayuwa ba tare da an kama shi ko tsare shi ba sai idan doka ta ba da damar hakan. Idan an kama mutum, dole ne a sanar da shi dalilin kamawar.

4) Haggi na Shari’a ta Adalci (sashi na 36)

Kowane mutum yana da haggin a saurari shari’arsa cikin gaskiya da adalci. Haka kuma, ana ɗaukar mutum mara laifi ne har sai kotu ta tabbatar da laifinsa.

5) Haggi na Sirri (sashi na 37)

Doka ta kare sirrin rayuwar mutum, iyalinsa, gidansa da hanyoyin sadarwarsa. Ba a yarda a kutsa cikin sirrin mutum ba tare da dalilin doka ba.

6) Yancin Tunani, Lamiri da Addini (sashi na 38)

Kowane mutum yana da haggin zaɓar addininsa, canza shi idan ya ga dama, da gudanar da ibadarsa cikin lumana.

7) Yancin Faɗar Albarkacin Baki (sashi na 39)

Kowane mutum yana da haggin bayyana ra’ayinsa da kuma neman ko yaɗa bayanai, muddin hakan bai saɓa wa doka ba.

8) Yancin Taro da Ƙungiya (sashi na 40)

Mutane suna da haggin yin taro cikin lumana da kuma kafa ko shiga ƙungiyoyi kamar jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin ma’aikata da sauran ƙungiyoyi na halal.

9) Yancin Zirga-zirga (sashi na 41)

Kowane ɗan Najeriya yana da haggin yin tafiya cikin ƙasar, zama a duk inda ya ga dama, da kuma fita ko dawowa Najeriya.

10) Yanci daga Nuna Bambanci (sashi na 42)

Ba a yarda a nuna wa kowa wariya saboda ƙabila, addini, jinsi, asalin haihuwa ko ra’ayin siyasa.

11) Haggi na Mallakar Gidaje da Filaye (sashi na 43)

Kowane ɗan Najeriya yana da haggin mallakar gida ko fili a ko’ina cikin ƙasar bisa tanadin doka.

12) Kariya ga Dukiya (sashi na 44)

Ba a yarda gwamnati ta ƙwace wa mutum dukiyarsa ba sai bisa tanadin doka, kuma dole ne a biya shi diyya idan doka ta tanada.

13) Iyakance Wasu Haggogi (sashi na 45)

A wasu lokuta, gwamnati na iya iyakance wasu haggogi idan hakan ya zama dole domin kare tsaron ƙasa, zaman lafiya, lafiyar jama’a ko haggin sauran mutane.

14) Haggi na Neman Kariya daga Kotu (sashi na 46)

Idan an tauye wa mutum hagginsa, ko kuma yana ganin za a tauye masa shi, yana da damar zuwa Babbar Kotu domin neman adalci da kariya.

Waɗannan haggogi su ne ginshigan kare mutunci da yancin ɗan Adam a Najeriya. Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya ba su kariya, kuma idan aka tauye su, mutum na da damar neman adalci a kotu. Sanin waɗannan haggogi yana taimaka wa kowa wajen kare kansa, mutuncinsa da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da mulki bisa adalci.

Domin karanta su da kuma fahimtar su yadda ya kamata ka je chapter 4 na 1999 constitution of the federal republic of Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button