Haqqoqin Dan Adam

Yakamata ka san kanka amma ta yaya?

Shin ko kun san Majalisar dinkin duniya ta yanke hukuncin kirkiran wasu dokoki wadanda suka kare haggin dan adam tare da fitar fa hakkoki wanda suke ganin ko wane dan Adam ya kamata ace yana da ita kuma baza a iya taba su ba balle takasu.

Shin waennen hakkoki ne wadannan?

To hakkoki ne guda talatin suka fidda gasu nan zan zayyano muku su;

1) Yancin Daidaito (Right to Equality ) Dukkan mutane an haife su cikin yanci kuma daidai suke a fannin mutunci da haggogi.

2) Yanci daga Nuna Bambanci (Freedom from Discrimination) Ba a yarda a nuna wa kowa wariya ko na launi ko na gabilanci ba

3) Yancin Rayuwa cikin Yanci da Tsaro (Right to Life and Liberty and Security ) Kowa na da haggin rayuwa da yanci da kuma samun kariya.

4) Yanci daga Bauta (Freedom from Slavery ) Bata yarda a mai da kowa bawa ko yi masa bautar dole ba.

5) ’Yanci daga Azabtarwa (Freedom from Torture ) Ba a yarda a azabtar da kowa ko a yi masa mugunta ko a wulakanta shi wurin mu’amala ba.

6) Haggin a Gane Ka a Gaban Doka ( Recognition Before the Law) Kowa na da haggin a amince da shi a matsayin mutum a gaban doka musali katin dan kasa

7) Daidaito a Gaban Doka (Equality Before the Law) Dukkan mutane daya suke a gaban doka.

8) Haggin Samun Adalci (Right to an Effective Remedy ) Kowa na da Haggin neman wakilci ko kariya idan an tauye masa Haggi.

9) Yanci daga Kama ko Tsare Ba Bisa Doka Ba (Freedom from Arbitrary Arrest or Detention) Ba a yarda a kama ko tsare mutum ba tare da wani dalili dokance ba.

10) Haggin Shari’a Mai Adalci (Right to a Fair Trial) Kowa na da Haggin a saurari shari’arsa cikin adalci.

11) Ana Daukar Mutum Mara Laifi Har Sai An Tabbatar da Laifinsa (Presumption of Innocence) Kowa mara laifi ne har sai kotu ta tabbatar da laifinsa a cikin kotu.

12) Haggin Sirri (Right to Privacy) Kowa na da Haggin kare sirrin rayuwarsa da na iyalinsa da kuma gidansa.

13) Yancin Zirga-zirga (Freedom of Movement ) Kowa na da kowa da Haggin yin tafiya cikin yanci kuma ya dawo daga tafiyar cikin yanci.

14) Haggin Neman Mafaka ( Right to Seek Asylum) Wanda ake zalunta na da Haggin neman mafaka a wata kasa.

15) Haggin kasancewa dan kasa (Right to a Nationality) Kowane mutum na da Haggin zama dan wata kasa.

16) Haggin Aure da Iyali (Right to Marry and Have a Family ) mutum na da Haggin yin aure da kafa iyali bisa dadaiton juna.

  1. Haggin Mallakar abin duniya (Right to Own Property) Kowane mutum na da Haggin mallakar dukiya.

18) Yancin Tunani da Lamiri da Addini (Freedom of Thought, Conscience, and Religion) Kowa na da yancin zaɓa da kuma bin addininsa.

19) Yancin Fadar Albarkacin Baki (Freedom of Opinion and Expression) Kowane mutum na da Haggin bayyana ra’ayinsa da kuma neman bayanai.

20) Yancin Taro da Ƙungiya (Freedom of Peaceful Assembly and Association) Kowa na da Haggin yin taro cikin lumana da shiga gungiyoyi.

21) Haggin Shiga Mulki (Right to Participate in Government) Kowa na da Haggin shiga harkokin gwamnati kai tsaye ko ta hanyar wakilai.

22) Haggin Tsaron Jin Daɗin Jama’a (Right to Social Security) Kowa na da Haggin samun tallafin jin daɗin rayuwa daga gwamnati ko ta wace hanya inde halattace ne.

23) Haggin Yin Aiki (Right to Work) Kowa na da Haggin yin aiki da kuma samun albashi mai adalci, da shiga ƙungiyar ma’aikata.

24) Haggin Hutu da Hutawa (Right to Rest and Leisure) Kowa na da Haggin samun lokacin hutu dakuma hutu na aiki.

25) Haggin Ingantacciyar Rayuwa (Right to an Adequate Standard of Living) Kowa na da Haggin samun abinci, tufafi, muhalli, lafiya da sauran bukatun rayuwa.

26) Haggin Ilimi (Right to Education ) Kowa na da Haggin samun ilimi. Ilimin firamare ya kamata ya kasance kyauta kuma wajibi.

27) Haggin Shiga Harkokin Al’adu da Kimiyya (Right to Participate in Cultural Life) Kowa na da Haggin cin gajiyar al’adu, fasaha da ci gaban kimiyya.

  1. Haggin Samun Tsari Mai Kare Waɗannan Haggin (Right to a Social and International Order) Kowa na da Haggin rayuwa cikin tsarin da zai tabbatar da waɗannan Haggogi.

29) Nauyin da Ke Kan Kowa Ga Al’umma (Duties to the Community) Kowa na da alhakin mutunta Haggin sauran mutane da kuma taimakawa ci gaban al’umma.

30) Ba a Yarda a Kwace Waɗannan Haggogi ba (Protection of These Rights) Babu wata gwamnati, ƙungiya ko mutum da ke da ikon soke ko kwace waɗannan haƙƙoƙin.

Shin kuna ganin ana sauke wadannan hakkokin ko kuma aa rubuta mana ra’ayinku a comment

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button